Skip to content

info@example.com

Treasure Hymns – Hausa

  • Home
  • Littafin Wakoki Hausa Hymns
  • Sample Page
  • Home
  • Littafin Wakoki Hausa Hymns
  • Sample Page

Hymn 89 Almasihu, Hasken Duniya Lyrics

  1. Home   »  
  2. Hymn 89 Almasihu, Hasken Duniya Lyrics

Hymn 89 Almasihu, Hasken Duniya Lyrics

January 10, 2026 treasurehymnsLittafin Wakoki Hausa Hymns

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 89 Almasihu, Hasken Duniya Lyrics

 

1
Almasihu, hasken duniya,
Begen dukan masu rai,
Yesu Rasul, Kalmar Allah,
Tun fiI azal kai kaɗai.
[Kai kaɗai madauwami ne,
Kai kaɗai maɗaukaki.] 2x

2
Kai ka ajiye rigar mulki,
Ka bar duk don cetonmu.
Zafin mutuwa ba ka ƙi ba,
Duk ka sha don ƙaunarmu.
[Karƃi yabo, karƃi mulki,
Naka ne har abada.] 2x

3
Mutuwa ta rasa iko
Bisanka, Mai Nasara.
Lahira ta buɗe ƙofa,
Ka shiga, har ka fita.
[An ɗauke ka can a Sama,
Aikinka ka gama nan.] 2x

4
Duk jama’a suna jiran
Zuwanka, ya Almasihu,
Duk Ekklesiya tana zarnan
Kewarka, Mai Cetonta.
[Zo da sauri, muna bege,
Zo, mu dinga ganinka.] 2x

5
Al’ummai, ku kasa kunne,
Shi ne Ubangijinku.
Ruhun Allah, jawo mutane
Zuwa sawun Mai Cetonsu,
[Ɗan Maryamu, Tsatson Dawuda,
Ibnu Llahi, Ɗan Mutum.] 2x

Post navigation

Previous: Hymn 343 Nigeria, We Hail Thee Lyrics
Next: Hymn 370 Allah Yana Gaba, Muna Bi Bayansa Lyrics

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent Posts

  • Hymn 346 A Cikin Farko Allah Ya Halitta Sama da Ƙasa Lyrics
  • Hymn 215 A Cikin Duniyan Nan Yanzu Lyrics
  • Hymn 218 A Cikin Dukan Halin da Mu Ke, da Murna Da Wahala Lyrics
  • Hymn 64 A Cikin Daren Nan da Aka Ba da Shi Lyrics
  • Hymn 347 A Cikin Farko Allahnmu Lyrics

Recent Comments

  1. A WordPress Commenter on Hello world!

Archives

  • January 2026

Categories

  • Littafin Wakoki Hausa Hymns
  • Uncategorized
Proudly powered by WordPress | Theme: goldy-mex by inverstheme.
Go to mobile version