Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 85 Raina Na Ba da Shi, Na Ba da Jinina Lyrics
1
Raina na ba da shi, na ba da jinina,
Jin daɗi duk na ƙi saboda ƙaunarka.
Raina na ba da shi, in ji Ubangiji,
2
Gidan Ubana can, gida mai daraja,
Na fito don in zo in zama talaka.
Na ba ka dukiyata, in ji Masoyinka.
3
Baƙunci mai wuya na haƙura da shi.
Kewa da ƙishiruwa, yunwa, gajiya, na ji.
Duk dominka na sha, in ji Mai Cetonka.
4
Ba za ka gane ba wahalar da na sha
Domin in ba ka rai, rai na har abada.
Da yardar rai na yi, in ji Maɗaukaki.
5
An fanshi naka rai da tamani mai yawa.
Nan gaba za ka kai wasu gun giciye.
Kai ne da nemansu, in ji Mai Cetonku.