Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 73 Jama’ar Ɗan Allah, Ku Taru Lyrics
1
Jama’ar Ɗan Allah, ku taru ku yi murna,
Ku taru, ku taru a Baitalahmi.
Zo mu gaishe shi, Sarkin mala’iku
KORUS
Mu yi masa sujada, mu yi masa sujada,
Mu yi masa sujada, Mai Cetonmu
2
Zo dai ku gan shi, jariri marar ƙarfi,
Yesu Ɗan Allah ne Madauwami.
Aka haife shi, ba a halicce shi ba.
Korus
3
Rundunan Sama, yi ta rera waƙa,
Can cikin Sama ku ke yabonsa,
Yabo ga Allah, yabo kuwa ga Ɗansa
Korus
4
I, Ubangiji, kai ne mu ke yabo
Gaisuwa mai gaskiya mu ke yi maka.
Kai, Kalmar Allah, cike da alheri
Korus