Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 62 Ya Ubangijinmu, Kalmarka Ta Dauwama Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 62 Ya Ubangijinmu, Kalmarka Ta Dauwama Lyrics

 

1
Ya Ubangijinmu, Kalmarka ta dauwama
Wajib ne a gaskata, a kuma karƃe ta.

2
Idan maƙiyanmu suna tsananta mana,
Maganar cetonka ita ce ƙarfinmu.

3
In wahala ta zo, ko masifa ta taso,
Haskenka zai bishe mu, za ya kiyaye mu.

4
Wa ya san misalin murna mafificiya
Ta miƙa bishararka zuwa mutanenka.

5
Jinƙanka ke ba da taimako ga masu rai,
Maganarka ta’aziyya ga wanda ke mutuwa.

6
Mu da muka gane tsarkin wannan Kalma,
Sai mu ƙaunace ka, don kullum mu bi ka.

Exit mobile version