Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 578 Yesu Na Naɗe Ka Sarkina Lyrics
1
Yesu na naɗe ka sarkina
Yi mulki cikina
Ka mallake ni duk yanzu
Yesu Mai Cetona.
2
Kada in manta da ƙamnarka
Wadda ta kai ga mutuwa
Kada in mance da wahalarka
Yesu Mai Cetona.
3
Ko cikin duniyan nan yanzu
In tuna da giciyenka
Da azabar rai da raɗaɗi
Yesu Mai Cetona.
4
Ina fa kyauta da zan yi yau,
Shaidar godiyata ?
Ni ba ka zuciya da raina duk,
Yesu Mai Cetona.