Skip to content

info@example.com

Treasure Hymns – Hausa

  • Home
  • Littafin Wakoki Hausa Hymns
  • Sample Page
  • Home
  • Littafin Wakoki Hausa Hymns
  • Sample Page

Hymn 53 Yesu Yana Jin Addu’a Lyrics

  1. Home   »  
  2. Hymn 53 Yesu Yana Jin Addu’a Lyrics

Hymn 53 Yesu Yana Jin Addu’a Lyrics

January 10, 2026 treasurehymnsLittafin Wakoki Hausa Hymns

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 53 Yesu Yana Jin Addu’a Lyrics

 

1
Yesu Yana jin addu’a,
Yesu Ubangijinmu,
Masu sonsa, masu binsa,
Su ne nasa cetattu.
Yawan sonsu a wurinsa!
Su ne tasa dukiya,
Yana zuba musu ido,
Yana ba su daraja.

2
Yesu yana yin addu’a,
Aikin ceto nasa ne,
Masu roƙo wurin Allah
Sai a cikin sunansa.
Shi jagora ne gare mu,
Ganin Allah sai da shi,
Yesu, shugaban sujadar
Da mutane za su yi.

3
Mu ma sai mu yi addu’a,
Almasihu yana nan.
Kalma tasa ta tabbata,
Shi zai yarda da roƙon.
Ya riga ya yi alheri,
Ya yi mana gafara.
Kyautarsa ta wadace mu
Har iyakar duniya.

4
Yesun nan, mai yin addu’a,
Allah ne ya ɗaukaka.
Kada kowa fa ya raina
Wanda shi ya girmama.
Wata rana in ya komo,
Gani kuwa zai kori ji,
Tuba dai, ka karƃi ceto
Tun da sauran zarafi.

Post navigation

Previous: Hymn 156 Zo Gare Ni, Masu Kaya Lyrics
Next: Hymn 190 Yesu Ya Zo Da Ƙaunarsa Lyrics

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent Posts

  • Hymn 346 A Cikin Farko Allah Ya Halitta Sama da Ƙasa Lyrics
  • Hymn 215 A Cikin Duniyan Nan Yanzu Lyrics
  • Hymn 218 A Cikin Dukan Halin da Mu Ke, da Murna Da Wahala Lyrics
  • Hymn 64 A Cikin Daren Nan da Aka Ba da Shi Lyrics
  • Hymn 347 A Cikin Farko Allahnmu Lyrics

Recent Comments

  1. A WordPress Commenter on Hello world!

Archives

  • January 2026

Categories

  • Littafin Wakoki Hausa Hymns
  • Uncategorized
Proudly powered by WordPress | Theme: goldy-mex by inverstheme.
Go to mobile version