Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 439 Kana da Kuɗi Lyrics
1
In kana da kuɗi, sai girman kai
Kana dubin fa ka fi kowa
Wanda ba shi da kana dubin ka fi shi
Tuna fa ƙarshen mu guda ne.
KORUS
Mine ne ka samu oh ya ɗan Adam
Wanda Allahnmu bai baka ba
Domin haka kawas da girman kai
Ka miƙa kanka ga Allah.
2
In kana da illimi sai girman kai
Kana dubin kowa jahili
Wanda ba shi da illimi ka raina shi
Tuna fa ƙarshen mu guda ne.
Korus
3
In kana da baiwa sai girman kai
Kana doro kana takama
Wanda ba shi da kana dubin ka fi shi
Tuna Ubangijinmu guda ne.
Korus
4
Allah ya bada baiwa ga kowane ɗayanmu
Domin aikinsa ya ci gaba
Abin da Allah ya baka ka yi aikinsa da shi
Gama Ubangijinmu guda ne.
Korus