Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 429 Je Gaya Bisa Tudu Lyrics
KORUS
Je shaida bisa tudu,
Cikin duniya da ko’ina.
Je shaida bisa tudu,
An haifi mai ceto
1
Makiyaya na tsaro
Garken su da dare.
Sun dubi cikin sama
Sun ga haske ƙwarai.
Korus
2
Makiyaya sun razana
A wurin da suke.
Mala’iku suna rera
Shelar ‘Bishara ne’.
Korus
3
” A cikin garin Dawuda
An haifi jaririri.
Shi ne mai ceton duniya
Ƙaunar Ubangiji”.
Korus