Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 423 In Na Yi Tunani Sosai Lyrics
1
In na yi tunani sosai
Kan zuwan Ubangijina
Da yadda ni zan tsaya dai
Ko murna ko kuwa hawaye.
KORUS
Yesuna, Yesuna,
Ka tsarkake ni tun yanzu,
Kada ka rage kome nan
Ya zama kaya na Shaiɗan
Yesuna, Yesuna
Ka tsarkake ni tun yanzu.
2
Kada a ranar zuwansa
Ya iske ni da zunubi
Lalle in ɓoye fuska ta,
In ce, “Ya Allah, me zan yi?”
Korus
3
Ran da ka kira ni in zo,
Domin ka gwada aikina,
Idan wuta ta cinye duk
Ina misalin kukata ?
Korus
4
Ya Yesu, ji addu’ata
Ka ba ni ƙargin zuciya
In kama aikinka sosai
In tarbe ka da daɗin rai.
Korus