Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 396 Da Hannuna Biyu Zan Yi Aikinka Lyrics
1
Da hannuna biyu zan yi aikinka
Baki zai yi ta yabonka.
Da kunnena biyu zan ji maganar
Murya ta riƙa rairawa.
KORUS
Ya Allah, ni na zo, amshi dukan rai na yau
Ya Allah, ni na zo, kada in ƙara zunubi.
2
Da ƙafa biyu na ka hanya
Zuwa gidanka can sama
Da ido zan karanta labarin
Yesu da dukan ƙamnarka.
Korus
3
Riƙe dukan zuciyata, ya Ruhu
Muryarka ina saurara,
Duk kwanakina zuwa mutuwa,
Ina so in yi shaida.
Korus