Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 349 A Cikin Mugunta An Yi Cikina Lyrics
1
A cikin mugunta an yi cikina
A ciki kuwa uwata ta haife ni.
Ҡamnar Yesu ta zo ta neme ni
Har ta bayyana mani dukan laifina.
KORUS
Musulmi da arna duk
Ku tuba tun yanzu
Gama ba daman tuba ranar shari’a.
2
Gama Yesu shi ba ya zaɓe ba
Baƙi, fari, ko kuwa rawaya ne
Ya mai da mu duka abokansa
Gama shi ba ya mai da kansa ya fi kowa.
Korus
3
Ekklisiya , mu ɗauki bishara,
Mu shiga cikin dukan ƙauyekan
Ga yamma suna ta mutuwa
Bari mu bar gida mu je, mu bishe su.
Korus
4
Ҡamnar Yesu ba za ta ƙare ba
Har wa yau ma tana a duniyan nan.
Domin ta ba mu Ruhu Mai Tsarki
Har shi taimake mu a cikin aikinsa.
Korus
5
Ku masu bi, mu yabi Mai Ceto
Mu shaida sunansa ga mutane
Mu yi ta ce, “Ga hanya zuwa rai
Gama ba wata hanyar ceto sai Yesu”.
Korus