Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 348 A Cikin Filibbiyawa Lyrics
1
A cikin Filibbiyawa
Sura ta uku kuwa,
Mu duba aya ta goma
Mu yi ta koyasuwa
KORUS
Don in sa Shi, Yesu Kristi,
Da ikon tashinsa
Da tarayyar raɗaɗinsa,
A cikin rain yau.
2
Ga ni, ana kamantad da ni,
Bisa ga mutuwarsa
Domin da ikonsa in kai
Ga tashin matattu.
Korus
3
Ban ce na rigaya na samu,
Ko kuwa na cika ba,
Amma in nace binsa
Don in sami rawani.
Korus
4
Ƴanuwa, ni ban maida kaina
Na zama cikakke,
Abubuwa na da na manta da su
Don in yi ta kutsawa.
Korus
5
Ina nan, ina nace binsa,
Har zuwa mutuwa
In kai ga ladan nasara,
Ta kiran Allahna.
