Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 346 A Cikin Farko Allah Ya Halitta Sama da Ƙasa Lyrics
1
A cikin farko Allah ya
Halitta sama da ƙasa.
Ta wurin ikon maganarsa
Duniya da kome sun zama.
KORUS
Mai iko, Mai iko
Allah ne Mai ikon kome,
Mai iko, Mai iko
Allah ne, Mai ikon dukan kome.
2
Ҡasa fa duka wofi ce
Duhu ya rufe ruwaye.
Rana ta fari Allah ya ce
Bari haske shi kasance.
Korus
3
Rana ta biyu Allah ya ce
Bari sarari ya kasance,
Kuma ya raba ruwaye
Haka ya zama gaba dai.
Korus
4
Rana ta uku tekuna
Sun tattaru wari ɗaya.
Ciyawa da itatuwa
Kowane masu bada ƙwaya.
Korus
5
Rana ta huɗu an gani
Can cikin sama haskoki
Bisa duniya su yi mulki
Rana da wata da tamrari.
Korus
6
Rana ta biyar Allah ya ce
Kifi su cika ruwaye,
Tsuntsayen sama su yalwaita,
Su haifu har duniya ta cika.
Korus
7
Rana ta shidda bisashe
Ya yi su, masu-rarrafe
Mutum da mananinsa ne
Haka ya gam aikin ne.
Korus
8
Rana ta bakwai Allah fa
Ya huta daga aikinsa
Haka mu kuma ƴayansa
Mu huta rana guda kuwa.
Korus