Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 339 Uba Na Sama, Allahnmu, Ka Dubi Ƙasarmu Lyrics
1
Uba na Sama, Allahnmu, ka dubi ƙasarmu,
Ka koya mana, ƴaƴanka, mu taya danginmu.
2
Ka sa mu bi tafarkinka, mu jawo kabilan nan,
Su riƙa ba da gaskiya, su karƃi mulkinka.
3
Ya Allah, ba mu ikonka, mu tsare gaskiya,
Mu kafa. shari’a daidai, mu hana rikici.
4
Ka koya mana dokoki, mu cika wa’adi,
Mu zauna lafiya da duk jama’a ta ƙasarmu.
5
Nan gaba za mu yabonka domin ka cece mu.
Kullum mu cika nufinka, mu yi ta aikinka.