Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 316 Duba Taron Nan Mai Girma Lyrics
1
Duba taron nan mai girma
Wanda ba mai ƙirgawa,
Suna tsaye gaban Allah,
Suna yabon sunansa.
Suna rera sabuwar waƙa,
Suna ta da murya,
Mulki, iko, girma, yabo,
Naka ne har abada.
2
Su waɗanda suka fito
Daga cikin tsanani,
Suka wanke tufafinsu
Cikin jinin Almasihu,
Suka jure, babu tsoro,
Suka raina mutuwa,
Sun ci nasara kan Shaiɗan
Cikin ƙarfin Ahmasihu.
3
Domin wannan, gaban Allah,
Yafaffu da cetonsa,
Suna yi masa sujada
Kullum, ba mai fasawa.
Yunwa, ba sa jinta kuma,
Yesu yana kiwonsu,
Shi ya shafe hawayensu
Daga dukan idanu.
4
Almasihu, muna roƙo,
Ubangijin tsarkaka,
Taimake mu cikin duniya
Mu bi sawun shaidunka.
Haka za mu ratsa mutuwa,
Za mu shiga mulkinka,
Inda Masu Binka duka
Su ke yabon ƙaunarka.