Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 296 Ina Son Mai Ceto, Yesu Lyrics
1
Ina son Mai Ceto, Yesu,
Ƙaunarsa ce zancena,
Ina murna domin giciyen,
Can ya kau da laifina.
KORUS
Ina waƙar Almasihu,
Jininsa ne fansata,
Tashinsa ne shaidar ceto,
Babu sauran la’ana.
2
Ina cikin bautar Shaiɗan,
Yesu ya ji tausayina,
Sai ya zo ya ba da ransa,
Yesu, ba mai kamarka.
Korus
3
Ina ɗaukaka sunansa,
Ƙarfin mutuwa ya ci,
Har ya sa in yi tarayya
Cikin nasara da shi.
Korus
4
Ko a can a gunsa zaune,
Ko a duniya saukakke,
Kauna ce ta haɗa ranmu,
Ni da Yesu ɗaya ne.
Korus