Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 283 Yesu Mu Ne Naka, Kai Ka Saye Mu Lyrics
1
Yesu mu ne naka, kai ka saye mu,
Ga kuwa muna zuwa bayanka yanzu.
Inda za ka duka, wurin za mu bi,
Kome wuyar aiki, lalle za mu yi.
Kome ya same mu, ko a cikin rai,
Ko ya kai ga mutuwa, Yesu mu ke bi.
2
Masu Bi, ku tashi, yi da zuciyarku,
Aikin Ubangiji yana jiranku.
Ga mutanen duniya, duhu su ke bi,
Ba sa bin tafarki, ƙaƙa za mu yi ?
Lalle sai mu tashi, hutu sai mu ƙi,
Har labarin Yesu dukansu sun ji.
3
Duba can a Sama, ga mazuninmu,
Daraja da tsarki, ba misalinsu.
Babu saura kewa, babu rabuwa,
Babu sauran cuta, babu mutuwa.
Gaba dai, ƴanuwanmu, yad da duniya,
Sama mu k enema, gidan tsarkaka.
4
Kome daɗin Sama, wanna ne mai fi,
Yesu za mu gani, Yesu za mu ji.
Ƙafa, hannu, goshi, shaida su ke yi
Da azabar kansa fansarmu ya yi.
Sauri fa, jama’a, babu hutawa!
Yesu mu ke nema, za mu wurinsa.