Skip to content

info@example.com

Treasure Hymns – Hausa

  • Home
  • Littafin Wakoki Hausa Hymns
  • Sample Page
  • Home
  • Littafin Wakoki Hausa Hymns
  • Sample Page

Hymn 256 Ya Mai Ceton Duniya Duka Lyrics

  1. Home   »  
  2. Hymn 256 Ya Mai Ceton Duniya Duka Lyrics

Hymn 256 Ya Mai Ceton Duniya Duka Lyrics

January 10, 2026 treasurehymnsLittafin Wakoki Hausa Hymns

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 256 Ya Mai Ceton Duniya Duka Lyrics

 

1
Ya Mai Ceton duniya duka,
Kasa mana kunnenka.
Bayinka fa, muna roƙo,
Muna neman ikonka.
Ba don kanmu mu ke so ba.
Ko’ina ga ƴanuwa.
Mu mun samu, su sun rasa.
Nuna mu su cetonka.

2
Mu da kanmu dai mun kasa,
Ikon ceto naka ne.
Ban da kai, ya Ubangiji,
Aikinmu na banza ne.
Ɗibo mana iko naka,
Cika mu da ƙarfinka.
Kullayaumin taimake mu,
Har mu gama aikinka.

3
Inda za mu shiga duka,
Taimake mu, bayinka,
Domin masu ji su yarda
Da labarin ƙaunarka.
Ƙarfafa ma’aikatanka,
Sa musu albarkarka,
Har mutane duk su tsira,
Duk su shiga mulkinka.

Post navigation

Previous: Hymn 199 Ya Ruhun Allah, Zo Yanzu Lyrics
Next: Hymn 253 Ya Allahna, Ƙarfafa ni Lyrics

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent Posts

  • Hymn 346 A Cikin Farko Allah Ya Halitta Sama da Ƙasa Lyrics
  • Hymn 215 A Cikin Duniyan Nan Yanzu Lyrics
  • Hymn 218 A Cikin Dukan Halin da Mu Ke, da Murna Da Wahala Lyrics
  • Hymn 64 A Cikin Daren Nan da Aka Ba da Shi Lyrics
  • Hymn 347 A Cikin Farko Allahnmu Lyrics

Recent Comments

  1. A WordPress Commenter on Hello world!

Archives

  • January 2026

Categories

  • Littafin Wakoki Hausa Hymns
  • Uncategorized
Proudly powered by WordPress | Theme: goldy-mex by inverstheme.
Go to mobile version