Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 236 In San Ka, Yesu, Na Ke So Lyrics
1
In san ka, Yesu, na ke so,
Da ikon tashinka yanzu.
In yi tarayya tare da kai
A cikin naka raɗaɗi.
2
A iske ni a cikinka,
Ba da adalcin kaina ba,
Amma ta wurin bangaskiya
Kullum in aikata nufinka.
3
Na duba ribar duniya,
Ba za ta isa dogara ba,
Dukan abu na lassafta
Hasara domin saninka.
4
Na baya sai in manta fa,
In kai ga ladan nasara.
Ya Yesu, sai in nace bi
Tare da kai, Ubangiji.