Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 224 Yesu Mu Ke So Don Ya Cece Mu Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 224 Yesu Mu Ke So Don Ya Cece Mu Lyrics

 

1
Yesu mu ke so don ya cece mu,
Muna jingina ga ƙirjinsa.
Shi ya mutu dai don mu sami rai,
Muna murna cikin cetonsa.

KORUS
Yesu …….Yesu ……
Ƙaunar Yesu mai girma ce.
Yesu ……. Yesu …….
Yesu ya mutu domin laifinmu.

2
Yesu mu ke bi har mutuwarmu,
Muna dogara ga ikonsa.
Shi ya tsare mu daga mugunta,
Muna murna cikin ƙaunarsa.
Korus

3
Shi mai ba da rai na har abada,
Muna jingina ga hannunsa.
Shi ya zaƃe mu daga duniya,
Muna murna cikin ikonsa.
Korus

Exit mobile version