Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 201 Ruhun Iko, Zo Gare Mu Lyrics
1
Ruhun iko, zo gare mu,
Mun ga kasawarmu yau.
Rashin jinƙai, rashin ƙauna
Rashin musun kanmu ma.
KORUS
Sai ka zo, ka tsarkake mu
Daga dukan kasawa.
Muna jira, muna jira,
Tsarkake mu duk yanzu.
2
Ruhun sani, zo gare mu,
Akwai duhu cikinmu.
Sanasshe mu, koya mana
Hanyar tsarkakewar rai.
Korus
3
Ruhun wuta, zo gare mu,
Kone duk muguntarmu
Har mu zama mutanenka
Cikin dukan gaskiya.
Korus
4
Ruhun haske da addu’a,
Bi da mu, ka ƙarfafa.
Muna bege, muna bege
Har mu sami nasara.
Korus
5
Ruhun ƙauna, zo gare mu,
Sai ka yafe mu yanzu.
Muna jira, muna kuka,
Amsa dai addu’armu.
Korus
6
Ƴanuwa, ku yafa Yesu,
Yafa sabon hali kuwa.
Yafa kuma zuciyar tausayi,
Ladabi da jurewa.
Korus
7
Ruhun Kristi, ni na gode,
Kana nan a zuclya,
Mallake ni, mallake ni
Daga yau har abada.
Korus