Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 185 Yesu Mai Ceto, Zo Wurinmu Lyrics
1
Yesu Mai Ceto, zo wurinmu,
Mu za mu bi ka har abada.
Kwashe zunubi, tsabtad da mu,
Ka ba mu rai na har abada.
KORUS
Yesu Mai Ceto, Mai Cetonmu,
Za mu yabe ka har abada.
Yesu Mai Ceto, Mai Cetonmu,
Mā ba ka girma har abada.
2
Yesu Mai Ceto, ka cece mu,
Ƙaunataccenmu har abada.
Magadan Sama, ka maishe mu,
Ƴaƴa na Uban har abada.
Korus
3
Yesu Mai Ceto, kai mu ke so,
Za ka karƃe mu har abada.
Kai, kana zuwa don Masu Bi,
Ma zauna tare har abada.
Korus