Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 173 Allah Ya Yi Alkawari Zancen Ceto Lyrics
1
Allah ya yi alkawari zancen ceto
Ga mai ba da gaskiya ga Ɗansa Yesu.
KORUS
Halleluya, an gama, ina ba da gaskiya,
An cece ni ta wurin jinin Yesu.
Halleluya, an gama, ina ba da gaskiya,
An cece ni ta wurin jinin Yesu.
2
Ko tafiyarmu tana da wuya a nan,
Lalle Yesu zai kai mu a wurinsa can.
Korus
3
Akwai waƙar da za mu yi cikin Sama,
Kuma yabonsa za mu yi har abada.
Korus