Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 141 Ga Duhu Dayawa A Duniyan Nan Lyrics
1
Ga duhu dayawa a duniyan nan,
Zunubi ya kawo duhu.
Amma hasken darajar Yesu ya zo,
Ya haskaka zukatanmu.
KORUS
Haske ya zo a duniyan nan,
Bari ya shiga zuciyarka
Dā, cikin duhu na ke, amma
Na zo wurin hasken Yesu.
2
Ba duhu a wurin Yesu, ko kaɗan,
Domin shi Mai Gaskiya ne.
Mu bi cikin haskensa, kusa da shi,
Zai haskaka zukatanmu.
Korus
3
Zunubi ya duhunta zuciyarka?
Ka zo wurin hasken Yesu.
Ka ba da gaskiya ga Yesu kaɗai,
Zai haskaka zuciyarka.
Korus
4
Akwai haske can cikin gidan Allah.
Ba duhu a cikin Sama,
Gama Almasihu shi ne haske can
A cikin gidan daraja.
Korus