Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 126 Ku Duba Irin Ƙaunan Nan, Ƙauna Ta Allahnmu Lyrics
1
Ku duba irin ƙaunan nan, ƙauna ta Allahnmu,
Domin mu zama ƴaƴansa, ya dinga ƙaunarmu.
2
I, domin wannan, duniyan nan ta riƙa raina mu,
Wahalarmu fa ɗaya ce da ta Ubangiji.
3
Yanzu mu ƴaƴan Allah ne, a cikin duniyan nan.
A rufe ya ke tukuna, zama na Sama can.
4
Mun sani ran da shi zai zo, ma zama kamarsa, Zai buɗe mana idanu, mu ga jamalinsa.
5
Wanda ya ke da begen nan kafe a bisansa.
Zai tsare tasa zuciya kamar Mai Cetonsa.