Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 115 Ya Yesu, Har Ga Mutuwa Ka Kai Don Cetonmu Lyrics
1
Ya Yesu, har ga mutuwa ka kai don cetonmu,
Ka ƙuje maƙiyinmu kuwa, ka ƃata ikonsa.
2
Ina misalin kayanka? Mai ɗauka, kai kaɗai!
Ka ɗauke namu zunubai, ta wurin giciyenka.
3
Yanzu ka hau ga Sama can, ka shiga hutawa.
Allah ya ba ka daraja a hannun damansa.
4
Me za mu kai guri Yesunmu? Mai fansarmu ne shi,
Baki ya kasa yabonsa, Yesu ne mafifici.
5
Mu miƙa ranmu gaba ɗaya, mu yi ta aikinsa,
Har ran da zai fyauce mu can a gidan Ubansa.