Skip to content

info@example.com

Treasure Hymns – Hausa

  • Home
  • Littafin Wakoki Hausa Hymns
  • Sample Page
  • Home
  • Littafin Wakoki Hausa Hymns
  • Sample Page

Hymn 347 A Cikin Farko Allahnmu Lyrics

  1. Home   »  
  2. Hymn 347 A Cikin Farko Allahnmu Lyrics

Hymn 347 A Cikin Farko Allahnmu Lyrics

January 10, 2026 treasurehymnsLittafin Wakoki Hausa Hymns

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 347 A Cikin Farko Allahnmu Lyrics

 

1
A cikin farko Allahnmu
Ya hallici dukan abu
Cikin sama da akan duniya
Dukan abin da kyau.

2
Ya hallici su mutane
Su Adamu, da Hawa’u
Ya sa su cikin gona ta Aidin
Su aikace ta kuwa.

3
Ya dokace su Adamu
Su Hawa’u kada su ci
Daga icce na tsakar gona
Ko mutuwa za su yi.

4
Shaiɗan ya shiga gonar nan
Ya jarabci Hawa’u dai
Ya sa ta shakkar maganar Allah
Ta bi maganarsa.

5
Ta ɗiba ɗiyan iccen nan.
Ashe, ta ci, ta ba miji
Sun ɓoye daga murya ta Allah
Sabo da tsoronsa.

6
Allah ya yi masu horo
Ga maciji, la’ananne ne shi
Mace ta haifa da baƙinciki
Wahala tata ce.

7
Da zufa bisa fuskarka
Ya Adamu, ka ci abincinka
Ҡasa ta haifi ƙayayuwa kuma
Zan kore ku da nan.

8
Allah ya kashe ɗan rago
Da fatarsa ya rufe wofinsu
Ya faɗa masu akwai Mai Zuwa
Mai Ɗauken laifofi.

9
Mun gaji halin Adamu
Duk mutane na duniya
Amma ya aiko Yesu Mai Ceto
Kama da ɗan rago.

10
An kashe Yesu Ɗan Allah
Da jininsa ya kwashe laifina
Yanzu na zama ta Allah kuma
Ta wurin bangaskiya.

11
Na gode maka ya Allah
Don ƙamnarka, don gafara
Ka taimake ni, in bi ka kullum.
Da zuciya ɗaya fa, Allahna.

Post navigation

Previous: Hymn 180 A Cikin Yesu Na Sami Rai, A Cikinsa Kaɗai Lyrics

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent Posts

  • Hymn 346 A Cikin Farko Allah Ya Halitta Sama da Ƙasa Lyrics
  • Hymn 215 A Cikin Duniyan Nan Yanzu Lyrics
  • Hymn 218 A Cikin Dukan Halin da Mu Ke, da Murna Da Wahala Lyrics
  • Hymn 64 A Cikin Daren Nan da Aka Ba da Shi Lyrics
  • Hymn 347 A Cikin Farko Allahnmu Lyrics

Recent Comments

  1. A WordPress Commenter on Hello world!

Archives

  • January 2026

Categories

  • Littafin Wakoki Hausa Hymns
  • Uncategorized
Proudly powered by WordPress | Theme: goldy-mex by inverstheme.
Go to mobile version