{"id":311,"date":"2026-01-10T12:03:14","date_gmt":"2026-01-10T12:03:14","guid":{"rendered":"https:\/\/treasurehymns.com\/hau\/uncategorized\/hymn-492-mutane-sun-far-yawaita-a-duniya-lyrics\/"},"modified":"2026-01-10T12:03:14","modified_gmt":"2026-01-10T12:03:14","slug":"hymn-492-mutane-sun-far-yawaita-a-duniya-lyrics","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/treasurehymns.com\/hau\/littafin-wakoki-hausa-hymns\/hymn-492-mutane-sun-far-yawaita-a-duniya-lyrics\/","title":{"rendered":"Hymn 492 Mutane Sun Far Yawaita a Duniya Lyrics"},"content":{"rendered":"<h2>Littafin Wakoki Hausa Hymns<\/h2>\n<h2><\/h2>\n<h2>Hymn 492 Mutane Sun Far Yawaita a Duniya Lyrics<\/h2>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>1<br \/>\n Mutane sun fara yawaita a duniya,<br \/>\n Sun cika \u0199asashe daga gabas har da yamma,<br \/>\n Kowa da sunansa da harshe dabam-dabam,<br \/>\n Sun bi ta hanyar duniya, sun mance da Uban.<\/p>\n<p> KORUS-1<br \/>\n Zan hallakada duniya,<br \/>\n In ji Ubangiji,<br \/>\n Zan aiki ruwan sama<br \/>\n Cikin wannan kwanaki.<\/p>\n<p> 2<br \/>\n Duk tunani da shawara \u01b4an Adam lala ne,<br \/>\n Ba wanda ya kula da abin da Allah ya ce,<br \/>\n &#8220;Na tuba da na yi mutum da dukan masu rai.<br \/>\n Zan shafe su da dabbobi har dukan tsuntsaye.&#8221;<br \/>\n Korus-1<\/p>\n<p> 3<br \/>\n Akwai mutum, sunansa Nuhu, mai adalci ne,<br \/>\n Ya sami tagomashi a gaban Ubangiji,<br \/>\n Kullum yana tafiya tare da Allah ne,<br \/>\n Tare da shi Allah ya yi babban alkawali.<\/p>\n<p> KORUS-2<br \/>\n Ka shiga cikin jirgi,<br \/>\n Da kai da \u01b4a\u01b4anka,<br \/>\n Zan hallakada duniya<br \/>\n Da ruwan tufana.<\/p>\n<p> 4<br \/>\n Shakara \u0257ari biyu Nuhu ya yi ta wa&#8217;azi<br \/>\n Ya yi ta shirya jirgi ko bai gane da abin,<br \/>\n Mutane sun yi dariya. &#8220;Ya hauka&#8221; duk sun ce,<br \/>\n Amma Nuhu bai kula ba, biyayya shi ke dai.<br \/>\n Korus-2<\/p>\n<p> 5<br \/>\n Nuhu ya bi\u0257a bisashe da tsuntsaye biyu biyu,<br \/>\n Sun shiga cikin jirgin nan tare da \u01b4a\u01b4ansa,<br \/>\n Allah ya rufe \u0199ofa, ruwan tsufana ya zo,<br \/>\n Ya rufe fuskar duniya har dukan duwatsu.<\/p>\n<p> KORUS-3<br \/>\n Mutane duk sun mutu,<br \/>\n Don ba su tuba ba,<br \/>\n Amma ya ceci Nuhu<br \/>\n Don ya bada gaskiya.<\/p>\n<p> 6<br \/>\n Ku mutane ku saurara abin da ya faru,<br \/>\n Ku juyo daga duhunku, ku tuba tun yanzu,<br \/>\n Ku  shiga cikin \u0199amnar Yesu, ro\u0199i gafara,<br \/>\n Allah za ya ji ku, za ya bu\u0257e \u0199ofa kuwa.<\/p>\n<p> KORUS-4<br \/>\n Ku shiga cikin jirgi,<br \/>\n Bai rufe \u0199ofa ba,<br \/>\n Amma idan kun kira<br \/>\n Lalle za ku yi makara.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Littafin Wakoki Hausa Hymns Hymn 492 Mutane Sun Far Yawaita a Duniya Lyrics &nbsp; 1 Mutane sun fara yawaita a duniya, Sun cika \u0199asashe daga gabas har da yamma, Kowa da sunansa da harshe dabam-dabam, Sun bi ta hanyar duniya, sun mance da Uban. KORUS-1 Zan hallakada duniya, In ji Ubangiji, Zan aiki ruwan sama [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":1,"featured_media":0,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"footnotes":""},"categories":[115],"tags":[],"class_list":["post-311","post","type-post","status-publish","format-standard","hentry","category-littafin-wakoki-hausa-hymns"],"amp_enabled":true,"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/treasurehymns.com\/hau\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/311","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/treasurehymns.com\/hau\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/treasurehymns.com\/hau\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/treasurehymns.com\/hau\/wp-json\/wp\/v2\/users\/1"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/treasurehymns.com\/hau\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=311"}],"version-history":[{"count":0,"href":"https:\/\/treasurehymns.com\/hau\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/311\/revisions"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/treasurehymns.com\/hau\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=311"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/treasurehymns.com\/hau\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=311"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/treasurehymns.com\/hau\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=311"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}