Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 232 Mai Kiwona Shi Yesu Ne Lyrics
1
Mai kiwona shi Yesu ne,
Duk tsoro dai ya kawu.
Ni ba zan rasa kome ba,
Ga kulawa mai kyau fa!
2
Abinci dai a yalwace,
Ga ruwan sha domina.
Ban rasa kome ba domin
Yesu ne makiyayi.
3
Har raina ma ya wartsake.
Yanzu dai Yesu ya sa
Shawararsa ta bi da ni
A duk tafiyata ma.
4
Har cikin kwarin mutuwa,
In dai ya sa in je can,
Tafiya tare mu ke yi,
Zai tsare ni sosai kuwa.
5
A idon su maƙiyana
Abinci ma ya shirya.
Da mai ya shafe kaina har
Sai daɗi na ke ta ji.
6
Alheri duk da jinƙansa
Yesu ya sa su bi ni.
Don haka daɗi na ke ji
Kullum a wannan duniya.
7
Mai kiwona shi Yesu ne,
Ba fashi, ko kaɗari ma,
Har gidansa madauwarni,
Mu je mu zauna tare.