Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 99 Akwai Sunan Nan Mai Daɗi Wanda Ba Mai Kamarsa Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 99 Akwai Sunan Nan Mai Daɗi Wanda Ba Mai Kamarsa Lyrics

 

1
Akwai sunan nan mai daɗi wanda ba mai kamarsa,
Wato sunan Ubangiji, begen dukan Masu Bi.

KORUS
Sunan nan, Yesu ne, sunansa da daɗin ji,
Sunan nan, Yesu ne, begen dukan Masu Bi.

2
Tun da na ji sunan Yesu, murna na ke yi sosai.
Wurinsa na sami ceto, gafara da kwanciyar rai.
Korus

3
Cikin sunan nan mai girma, a ke samun ceto fa,
Cikinsa a ke sujada, cikinsa a ke addu’a.
Korus

4
Sunan nan ya buɗe ƙofa, zuwa Allah Ubansa,
Gama ban da sunan Yesu, Allah ba za ya ji mu ba.
Korus

Exit mobile version