Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 98 Da Suna Wanda Ba Mai Fi A Dukan Zamanai Lyrics
1
Da suna wanda ba mai fi a dukan zamanai,
Yesu ne, marar zunubi, Ɗan Allah, shi kaɗai.
2
Allah ya sanya sunan nan kan sauran sunaye.
Mu yabe shi da rairawa, mu gusa gun kursiyi.
3
Mai kayan tulin laifofi shi faɗi sunan nan,
A cikinsa ga gafara, ba shakka, ko kaɗan.
4
Sunan, idan ka faɗe shi, an ji addu’arka.
Laifinka ba ya dubawa, sai jinin giciyensa.