Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 96 Babu Sunan da Ya Fi Sunan Yesunmu Lyrics
1
Babu sunan da ya fi sunan Yesunmu.
Shi ne wanda suka ƙi cikin fushinsu.
Sunan Yesu ba mai fi, Allah ne ya shaida shi.
2
Babu daɗin da ya fi daɗin sunansa.
Babu ceto, babu rai, sai a wurinsa.
Sama, duniya, Lahira Suna yabon sunansa.
3
Babu girman da ya fi girman sunansa.
Sarkin Sarakuna shi, Mai Shari’a kuwa.
Iko duka nasa ne, shi kaɗai mai mulki ne.
4
Sunan Yesu, ba mai fi cikin duniya.
Kan Ekklesiya ne shi, hasken Sama kuwa.
Iko, girma, ɗaukaka nasa ne har abada
