Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 95 Hosanna Ga Ɗan Dawuda! Mai Albarka Ne Shi Lyrics
1
Hosanna ga Ɗan Dawuda! Mai albarka ne shi
Wanda ke zuwa cikin sunan Ubangiji.
Kai Sarkin Isra’ila, shafaffen Allahnmu,
Cikin sunan Maɗaukaki, ka zo ka cece mu.
2
Hosanna ga Ɗan Dawuda! Mai albarka ne shi
Wanda ke zuwa cikin sunan Ubangiji.
Mutanen da sun ɗiba gazarin dabino,
Sun shimfiɗa a hanyarka domin ka taka su.
3
Hosanna ga Ɗan Dawuda! Mai albarka ne shi
Wanda ke zuwa cikin sunan Ubangiji.
Yau dukan jama’arka sun kawo yabonsu,
Domin su gai da sarkinsu wanda ya fanshe su.
4
Hosanna ga Ɗan Dawuda! Mai albarka ne shi
Wanda ke zuwa cikin sunan Ubangiji.
Ka shiga Birnin Ƙudus, ya kai mai nasara,
Tawali’u da yardar rai sun kai ka mutuwa.
5
Hosanna ga Ɗan Dawuda1 Mai albarka ne shi
Wanda ke zuwa cikin sunan Ubangiji.
Loton da ka ke duniya, wahala ce ka sha,
A hannun daman Allah, aka ba ka ɗaukaka.
6
Hosanna ga Ɗan Dawuda! Mai albarka ne shi
Wanda ke zuwa cikin sunan Ubangiji.
Ya Yesu Almasihu, Allah Maɗaukaki,
Kai ne Mai Ceton duniya, ya kai Mai Tsarki.