Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 93 Ku Mutanen Almasihu Lyrics
1
Ku mutanen Almasihu,
Rera waƙa, dukanku.
Sai ku faɗa wa jama’a
Duk labarin cetonku.
Albishir ne, Maryamu
Ta haife shi, Ɗan Mutum,
Sai fa godiya ga Allah
Domin duk alherinsa.
2
Sa’an nan ya ƙara girma.
Cike da tagomashi,
Shi Ɗan Allah yana koya
Mana hanyar adalci.
Idan mu amintattu ne,
Idan mun bi sawunsa,
Za ya kai mu wurin Uba,
Za mu sadu wurinsa.
3
Wajibi ne sai mu bi shi,
Domin yawan ƙaunarsa.
Shi ya sha wahalar giciye,
Ba don ya yi laifi ba.
Laifofin jama’a duka
Suka kai shi mutuwa.
Ƙofar rai ce shi ya buɗe
Don ya kai mu fadarsa,
4
Sai in yi masa sujada,
Allahna da Sarkina.
Sai in bauta masa kullum
Da iyakar ƙarfina.
Sai da dukan hankalina,
Sai da dukan zuciyata,
Zan bi Yesu, Mai Cetona,
Cikin ikon Ruhunsa.