Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 92 Wanene A Daki Can Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 92 Wanene A Daki Can Lyrics

 

1
Wanene a daki can,
Makiyaya gabansa?

KORUS
Shi ne Ubangiji Yesu!
Shi ne Sarki mai daraja!
Sai mu durƙusa a nan,
Mu yabe shi, Mai Ceto.

2
Wanene a daji ai,
Yana shan jaraba dai?
Korus

3
Yabon wa a ke ta yi
Domin duk alherinsa?
Korus

4
Wanene ke warkar da
Masu ciwo dayawa?
Korus

5
Wanene Mai Ta’aziyya
Domin masu ƃacin rai?
Korus

6
Wanene mai wa’azi
Ko’ina a Galili?
Korus

7
Wa ya je da dare kuwa
Zuwa gona don addu’a?
Korus

8
Wanene kan giciye
Zafin mutuwa ya ke ji?
Korus

9
Wanene ya tashi kuwa
Daga cikin kabari?
Korus

10
Wanene Mai Taimako
Shi kaɗai kuwa Mai Ceto?
Korus

11
Wanene a kursiyi
Mai Iko, Maɗaukaki?
Korus

Exit mobile version