Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 9 Ina Misalan Daraja Da Ban Mamaki Lyrics
1
Ina misalan daraja da ban mamaki da
Jamalinka ya bayyana, ya Allah, haskena!
2
Ya Allahna Madauwami, kwarjininka ya sa
In yi maka sujada fa a cikin zuciyata.
3
In ƙaunace ka kullum kuwa, mai iko duka ne,
Don ka yarda ka zo guna, ka nemi ƙaunata.
4
Ba wani uba na duniya, ba wata uwa kuwa,
Da za su iya renonmu yadda ka ke mana.
5
Sai abu ɗaya na ke so, in zauna gabanka,
In ga jamalin haskenka, in dinga sujada.
6
In yi shelar sunanka dai, in riƙa tunani
Yadda ka ƙaunace ni kuwa, ya Allah mai jinƙai.
7
Ina misalin daraja da ban mamaki kuwa
Na tsarin dukan hikima wadda ka ayana.
