Skip to content

info@example.com

Treasure Hymns – Hausa

  • Home
  • Littafin Wakoki Hausa Hymns
  • Sample Page
  • Home
  • Littafin Wakoki Hausa Hymns
  • Sample Page

Hymn 88 Ubangiji, Muna Gaisuwa Lyrics

  1. Home   »  
  2. Hymn 88 Ubangiji, Muna Gaisuwa Lyrics

Hymn 88 Ubangiji, Muna Gaisuwa Lyrics

January 10, 2026 treasurehymnsLittafin Wakoki Hausa Hymns

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 88 Ubangiji, Muna Gaisuwa Lyrics

 

1
Ubangiji, muna gaisuwa,
Mun gaishe ka, Sarkinmu,
Kai mai shan wahala tamu,
Kai mai cika cetonmu,
Kai, bayanin ƙaunar Uba,
Yesu, Dan Maɗaukaki,
Naka suna mu ke kira,
Yesu Ubangijinmu.

2
Kai ka kau da zunubanmu,
Rauninka dominmu ne,
Mutuwarka ta sayi ranmu,
Kai ne Mai Cetonmu dai.
Can dominmu ka ke roƙo,
Kana shirin gidanmu,
Kana jiranmu da ƙauna,
Yesu Ubangijinmu.

3
Kome girman sunan kowa,
Ba zai kai ga naka ba.
Kome yawan daɗin duniya
Ba ya kai ga daɗinka.
Baki ba ya iya faɗi,
Kunne ba ya iya ji,
Ko misalin naka daɗi,
Yesu Ubangijinmu.

4
Tara manyan duniya duka,
Duk da yawan girmansu,
Har mala’iku na Sama,
Ba su kai ka girma ba.
Ko har abada bayinka
Muna yi ta yabonka,
Dukan yabo sai ya kasa,
Yesu Ubangijinmu

Post navigation

Previous: Hymn 526 Ubangiji Shina Ta Biɗa Lyrics
Next: Hymn 272 Ta da Ido, Ka Duba Gonaki Lyrics

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent Posts

  • Hymn 346 A Cikin Farko Allah Ya Halitta Sama da Ƙasa Lyrics
  • Hymn 215 A Cikin Duniyan Nan Yanzu Lyrics
  • Hymn 218 A Cikin Dukan Halin da Mu Ke, da Murna Da Wahala Lyrics
  • Hymn 64 A Cikin Daren Nan da Aka Ba da Shi Lyrics
  • Hymn 347 A Cikin Farko Allahnmu Lyrics

Recent Comments

  1. A WordPress Commenter on Hello world!

Archives

  • January 2026

Categories

  • Littafin Wakoki Hausa Hymns
  • Uncategorized
Proudly powered by WordPress | Theme: goldy-mex by inverstheme.
Go to mobile version