Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 87 Ku Masu Ƙaunar Yesu Fa, Jama’ar Masu Bi Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 87 Ku Masu Ƙaunar Yesu Fa, Jama’ar Masu Bi Lyrics

 

1
Ku masu Ƙaunar Yesu fa, jama’ar Masu Bi,
Ku kasance da halin da ya zauna cikinsa.

2
Ko cikin surar Allah, shi, girmansu ɗaya ne,
Ya ƙanƙantad da kansa, har ya zama bawa, shi

3
Ya zama gurbinmu a nan, ya yi biyayya, shi,
Biyayya har ga mutuwa, mutuwar giciye.

4
I, domin wannan Allah kuwa ya ƙara girmansa,
Ya ba shi suna mafi kyau a bisa kowanne.

5
I, domin girman sunan nan, sunansa mafi kyau,
Gwiwoyin dukan masu rai duk za su rusuna.

6
Kowane harshe cikinsu zai yi shaidar Yesu,
Cewa shi Ubangiji ne don girman Allahnmu.

Exit mobile version