Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 86 Yesu Ya Bar Samaniya Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 86 Yesu Ya Bar Samaniya Lyrics

 

1
Yesu ya bar Samaniya,
Yesu ya shigo duniya,
Yesu ya ji tausayina,
Mai Cetona!

2
Yesu ya ɗauke laifina,
Yesu ya sha wahalata,
Yesu ya mutu domina,
Mai Cetona!

3
Allah bai ƙyale Ɗansa ba,
Allah ya ta da baransa,
Kuma ya kai shi gidansa,
Mai Cetona!

4
Yesu ya ba ni cetonsa,
Kada in ƙara zunubi.
Nan gaba sai in riƙa bin
Mai Cetona!

5
Yesu, da ni da shi, an ce
Allah ya haɗa mu sosai,
Shi ne ya kauda tsorona,
Mai Cetona!

6
Yesu zai komo duniya,
Aikinsa duk zai ƙarasa.
Na sa zuciya ga ganinsa,
Mai Cetona!

Exit mobile version