Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 84 Ga Labarin Daren Nan Lyrics
1
Ga labarin daren nan,
Ƙasar can
Aka haifa mana Ɗa.
Sai mu yi ta murna, murna,
Sai mu yi ta murna, murna,
Aka haifa mana Ɗa,
Cikin ƙasar gabas can.
2
Shi ne kyautar Allahnmu,
Dominmu,
Jariri Mai Cetonmu.
Lalle muna murna, murna
Lalle muna murna, murna.
Jariri Mai Cetonmu,
Kyautar Allah dominmu.
