Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 83 Makiyaya da Daddare Sun Tsare Garkensu Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 83 Makiyaya da Daddare Sun Tsare Garkensu Lyrics

 

1
Makiyaya da daddare sun tsare garkensu
Mala’ikan Allah ya zo, ya haskaka su fa.

2
“Kada ku ji tsoro,” ya ce, gama sun firgita,
“Labarin murna ne na kawo ga dukan duniya”.

3
“An haifi Almasihu yau, a birnin Dawuda fa,
Mai Ceto, Ubangiji ne, alamarsa ke nan”.

4
“Jariri za ku iske ma da siffar mutane
A nannaɗe da tsummoki cikin sakarkari.”

5
Da gama faɗin saƙon nan, taron haske ya zo,
Mala’iku ‘na rerawa, suna ta yin yabo.

6
“Ɗaukaka duk ga Allahnmu, salama ga duniya,
Aminci ga mutane duk, yanzu da koyaushe.”

Exit mobile version