Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 82 Yesu Rasul, Mai Alheri Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 82 Yesu Rasul, Mai Alheri Lyrics

 

1
Yesu Rasul, mai alheri,
Ɗan Maryamu, mai nasiha,
Haifuwarka ta ƙanƙanci,
Ba mu ruhun jurewa.

2
Ko a can sakarkarinka,
Ka zo ceton mutanenka
Cikin duniya ta baƙunci,
Karƃi mulkin zuciyarmu.

3
Kai mai fansar mutanenka,
Mai yin nasara da mutuwa,
Bar mu zauna kullayaumin
Kurkusa da kursiyinka.

4
Kai mai ɗaukar wahalarmu
Ka san dukan tunaninmu,
Bar mu sa ido gare ka
Don mu sami gaskiyarka.

5
Bishe mu, ya Ubangiji,
Kau da dukan mugun nufi,
Karƃi ranmu, mun roƙe ka,
Don mu aika nufinka.

Exit mobile version