Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 81 Ku Ji Muryar Annabci Kuwa, da Allah Ya Faɗa Lyrics
1
Ku ji muryar annabci kuwa, da Allah ya faɗa.
Ishaya ne ya ambata abin al’ajabi.
2
Ga shi an haifi yaro dai, mu aka bai wa Ɗa.
Sunansa. kuwa Al’ajabi, kuma Mai Shawara.
3
Allah mai iko duka kuwa, Madauwamin Uba,
Sarkin Salama, mulkinsa ba shi da iyaka.
4
A bisa kursiyin Dawuda, da bisa mulkinsa,
Zai kafa shi kan shari’a da kuma gaskiya.
5
Wannan, Allah mai runduna da himmarsa zai yi.
Maganarsa zai cika ta, alkawari ya yi.
6
Yau cikin birnin Dawuda fa aka haifi Yesu.
Mu tafi can sakarkari, sujada za mu yi.