Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 80 Dā, Mala’iku Ke Shaida Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 80 Dā, Mala’iku Ke Shaida Lyrics

 

1
Dā, mala’iku ke shaidar
Haihuwar Yesu Mai Ceto.
Ji labarin farinciki
Wanda shi ke dominku.

KORUS
Zo, ku yi masa sujada
Shi Sarkin Sarakuna.

2
Makiyaya suna tsaron
Garkensu da daren nan.
Haske ne ya kewaye su,
Aka shaida musu ma.
Korus

3
Masu hikima na duniya
Bar zurfin tunaninku.
Nemi ceto wurin Yesu,
Kuna jin labarinsa.
Korus

4
Sarakuna, talakawa
Malamai, almajirai
Mazaje da mata duka,
Tsofaffi da jarirai.
Korus

Exit mobile version