Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 79 Ya Ƙanƙanuwar Baitalahmi, Can Ƙasar Yahuda Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 79 Ya Ƙanƙanuwar Baitalahmi, Can Ƙasar Yahuda Lyrics

 

1
Ya ƙanƙanuwar Baitalahmi, can ƙasar Yahuda,
Ba auta ba ce ko kaɗan cikin Yahudiya,
Gama daga cikinki, Mai Ceto zai fito.
Tauraronsa a bisanki, shi kansa cikinki.

2
Hanyoyinki dā duhu ne, yanzu ga haskensu.
Dā, mutane sun raina ki, yanzu ga daraja.
Ji waƙoƙin mala’iku, yabo ga Allahnmu
A cikin mafi ɗaukaka, a duniya salama.

3
Shehunan gabas fa sun zo, sun kawo dukiya.
Gaisuwa, girma, daraja, ga yaron aka bayar.
Ga Yesu Mai Cetonmu a cikin Baitalahmi,
Ba waninsa a duniya, Maɗaukaki ne shi.

Exit mobile version