Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 77 Yara, Mu Tashi da Murna Mai Yawa Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 77 Yara, Mu Tashi da Murna Mai Yawa Lyrics

 

1
Yara, mu tashi da murna mai yawa,
Zo, za mu gai da Mai Cetonmu yau,
Ga shi a kwance, jariri ƙanƙane,
Tare da shanu a Baitalahmi can.

2
Taron mala’iku, ga su a Sama,
Waƙa mai daɗi kuwa su ke ta yi,
“Yaba ga Allah, a duniya salama.”
Zance mai faranta zuciya ne.

3
Hasken tauraron nan ne suka gani,
Shehunan gabas sun tashi, sun zo.
Kayan zinariya ne suka kawo,
Duk suka zuba gabansa kyauta.

4
Yesu mai sonmu, mu ƴaƴanka kuma,
Ga mu, mun taru da gaisuwarmu.
Lubban ka murru ba su ne muka kawo ba,
Kayan zinariya ba mu da su.

5
Mu dai, ga kayan da mu za mu kawo,
Ƙarfinmu, ƙaunarmu, zuciya da rai,
Duk mu ke ba ka, jariri, Mai Ceto,
Kai ne masoyinmu har abada.

Exit mobile version