Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 75 Mu Zo Mu Gai da Almasihu, Yesu Mai Cetonmu Lyrics
1
Mu zo mu gai da Almasihu, Yesu Mai Cetonmu.
An daɗe ana jiransa, ya ziyarto mu yanzu.
2
Ya zo da kalmar fansarmu, ya zo da gafara
Ku ɗaurarru da zunubi, ku rera sunansa.
3
Ya fito gidan Ubansa, ya zo da warkarwa.
Ku masu ciwon zuciya, ku sheka wurinsa.
4
Ba za mu daina yabo ba, ya Ɗan Mauɗaukaki,
Sai duniya duk da cikarta ta ji Iabarinka.
