Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 72 Yesu Ɗan Allah, Yau Ka Zo Lyrics
1
Yesu Ɗan Allah, yau ka zo!
Mu fa me za mu yi?
Mala’iku na sama, ku taimake mu waƙa.
Yanzu da asubahi, yanzu da asubahi.
Alhamdu ga Allah har abada!
2
Ya Almasihu, yau ka zo!
Mu fa me za mu yi?
Mu durƙusa gabanka, mu yi maka sujada,
Mu girmama sunanka, mu girmama sunanka.
Alhamdu ga Allah har abada!
3
Yesu jariri, Mai Ceto,
Mu ƴaƴanka mun zo,
Mu ƙanƙananan yara mun kawo maka ranmu
Mu sa maka albarka, mu sa maka albarka.
Alhamdu ga Allah har abada!
4
Baitalahmi ne zuciyata,
Ya Yesu, yau ka zo!
Ya Ruhu, ina roƙo, ka kawo shi a wurina
Ya zauna har abada, ya zauna har abada.
Alhamdu ga Allah har abada!