Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 7 Ya Allah, Kai Mai Girma Ne Lyrics
1
Ya Allah, kai mai girma ne, kai ne Maɗaukaki,
Sunanka dai mu girmama saboda jinƙanka.
2
Ya Allah, kai Madauwami, Alƙadiru ne kai.
Hikimarka da ikonka sun wuce saninmu.
3
Ya Allah, ina tsoronka, tsoro mai ladabi.
Sujada tawa da bege, tara da kuka ne.
4
Kaunar uwa ko ta uba, dabam da taka ce.
Ya Ubangiji, ƙaunarka ta fi ta duniya duk.
5
Na gode maka, Allahna, don irin ƙaunarka,
Tausayinka da hanƙurinka da ni, mai zunubi.
6
Ya Ubangiji, wane mu da za ka so mu fa?
Mun gode maka, ya Yesu don halin ƙaunarka.
7
Ran da ma duba fuskarka a cikin Sama can,
Ya Yesu, kai mai ƙaunarmu, sai murna za mu yi.
