Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 69 Yesu, Maganar Rai, Lura da Ni Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 69 Yesu, Maganar Rai, Lura da Ni Lyrics

 

1
Yesu, maganar rai, lura da ni.
Nan cikin duniya ga zunubi.
Shaiɗan da wayonsa ya ruɗe ni,
Zo nan da ikonka, ka cece ni.

2
Yesu, mai fansar rai, ka wanke ni
Da jinin sadaka mai tsarki.
Tun da ka ba da rai saboda ni,
Jawo ni wurinka, ka riƙe ni.

3
Yesu, gurasar rai, ba ni in ci
Yadda ka bayar da a Galili.
Ba ni da kome nan sai kai kaɗai,
Kullum ka cishe ni da jibin rai.

4
Yesu, mai ba da rai, tuna da ni.
Alherin halinka ya gamshc ni.
Zubo da Ruhunka, tsabtad da ni,
Har zan yi nasara da zunubi.

Exit mobile version